MediaOfIslam.Com

Latest

Post Top Ad

Post Top Ad

Mediaofislam.com

Tuesday, January 1, 2019

Hukuncin Sallah Kan Mashayin Giya

January 01, 2019 0
Assalamu Alaikum.
To Allah ya gafarta malam, wanda ya san wajibcin sallah da azumi akansa amma saboda ya taba jin fatawar cewa duk wanda yasha giya sai yayi kwana 40 ba’a ansar ibadar sa shi kuma baya kwana 40 baisha giya ba sai yabar sallah da azumi tsawon shekaru, yanzu kuma ya tuba ya bari ya ramuwar sallar da azumin da yabari zai kasance?
Related image
Wa’alaikumussalam
Amsa
Lallai hadisai sun nuna ba’a karbar sallar wanda ya sha giya ta kwana arba’in kamar yadda yazo cikin silsilah swahiha 709, hadisin ya nuna idan mutun ya tuba Allah zai yafe masa, saboda haka tunda ya tuba muna fatar Allah zai yafe masa, sai yaci gaba da istigfari da yawaita ibada,
Malamai sunyi sabani wajen ramakon sallah da azumi ga wanda yabar su baiyi har tsawo wani lokaci,  wasu sunce zai rama wannan shine ra’ayin Jamhurun malamai  waau kuma sunce ba zai rama ba don sun gina fahimtar su akan dalilai na shari’a da suka nuna kafurcin wanda yabar sallah, sannan suka ce in ance zai ya rama hakan ka iya wahalar dashi kila ya kasa ya koma gidan jiya,  suna hujja kuma da fadar cikin Suratul Ɗaha 11, da ta 82.
Don haka dai babu ramuwa akan sa sai istigfari da tsaida sallah da ci gaba da azumi da lazimtar ibada sosai da sosai, an tambayi malaman  lajna 6/41 hukuncin wanda yabar sallah da azumi sun bada fatawar ba zai rama ba.
Wallahu A’alam.
Malam Nuruddeen Muhammad Mujaheed
07/08/2016.
Daga : ZAUREN FIQHUS SUNNAH group.
Read More

Matsayin Sallah Da Hukuncinta

January 01, 2019 0

Bayani Mece ce Sallah



Ma’anar kalmar sallah a larabceIta ce «Addu’a»
Ma’anar Sallah a shari’anceIta ce bautawa Allah da zantuka da ayyuka kevantattu, waxanda ake buxe su da kabbara, a rufe su da sallama.

Image result for jumma prayer


Matsayin Sallah A Musulunci

1 – Sallah ita ce rukuni na biyu a rukunan musulunci,

Manzon Allah (S.A.W) ya ce, “An gina musulunci a bisa ginshiqai guda biyar, shaida wa babu abin bauta wa bisa cancanta sai Allah, kuma Muhammad bawansa ne Manzonsa ne, da tsayar da sallah…..” [Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi].

2 – Sallah ita ce mafi falalar ayyuka,

Manzon Allah (S.A.W) ya ce, “Mafi falalar ayyuka sallah a farkon lokacinta” [ Tirmizi ne ya rawaito shi].

3 – Sallah ce mararraba tsakanin musulunci da kafirci,

Annabi (S.A.W) ya ce, “Haqiqa tsakanin mutum da shirka da kafirci barin sallah” [Muslim ne ya rawaito shi].

4 – Sallah ita ce ginshiqin musulunci, a kanta ne – bayan tauhidi – aka gina musulunci,

Annabi yana cewa “Kan wannan lamari gabaxaya shi ne musulunci, ginshiqinsa kuwa sallah” [Ahmad ne ya rawaito shi]

Falalar Sallah

1 – Sallah haske ce ga ma’abocinta, Manzon Allah (S.A.W) ya ce, “Sallah haske ce” [Muslim ne ya rawaito shi].
2 – Sallah kaffara ce daga zunubai, Allah Maxaukakin sarki ya ce, “Ka tsaida sallah a gefen rana da wani yanki a cikin dare, haqiqa kyawawan ayyuka suna tafiyar da munana, wannan tunatarwa ce ga masu tunawa”(Hud: 114).
Manzon Allah (S.A.W) ya ce, “Ku bani labari da ace akwai qorama a qofar xayanku, yana wanka a cikinta a kowace rana sau biyar, shin wani abu zai ragu na dattinsa, sai suka ce “Babu wani dattinsa da zai ragu” sai Manzon Allah (S.A.W) ya ce, “Hakanan misalin salloli biyar suke, Allah yana goge zunubai da su” [Bukhari ne da Muslim ne suka rawaito shi].
3 – Sallah sababin shiga Aljannah ce, Manzon Allah (S.A.W) ya ce wa Rabi’a xan Ka’abu – yayin da ya roqe shi zama tare da shi a Aljannah – sai Manzon Allah ya ce masa “Ka taimaka mi a kan kanka da yawan sujjada (Watau sallah)” [ Muslim ne ya rawaito shi].

Hukuncin Sallah

Salloli guda biyar xin nan wajibi ne da Alqur’ani da Sunnah da Ijma’i.
1 – Dalili daga Alqur’ani :
Allah ya ce, “Ku tsayar da Sallah ku bada zakkah, ku yi ruku’u tare da masu ruku’u”(Albaqra : 43).
2 – Dalili daga sunnah :
Manzon Allah (S.A.W) ya ce, “An gina musulunci a kan ginshiqai biyar : Shaidawa babu abin bautawa bisa cancanta sai Allah, Kuma Muhammad Bawansa ne Manzonsa ne, da tsayar da sallah, da bayar da zakkah, da ziyartar xakin Allah, (Hajji) da azumin Ramadan” [Bukhari ne da Muslim ne suka rawaito shi].
– An karvo daga Xalhatu xan Ubaidillahi, ya ce, wani mutum ya tambayi Annabi (S.A.W) game da musulunci, Sai Manzon Allah (S.A.W) ya ce, “Salloli biyar a cikin yini da dare” Sai ya ce, “Shin akwai wasu daban a kaina ban da su?” Sai Manzon Allah ya ce, “A’a, sai dai ka yi nafila” [ Bukhari ne da Muslim ne suka rawaito shi].
3 – Dalili daga Ijma’i :
Al’umma gabaxayanta ta haxu a kan wajabcin salloli biyar a cikin yini da dare.

Su Waye Sallah Ta Wajaba A Kansu?

Sallah ta wajaba a kan dukkan musulmi, baligi, namiji ko mace.
Rama Sallah
Ba a umartar kafiri da rama abin da ya wuce shi na salloli kafin ya musulunta, saboda musulunci yana shafe abin da yake gabaninsa.

Hukuncin Wanda Baya Sallah

1 – Wanda Ba Ya Sallah, Kuma Yana Inkarin Wajabcinta :

A sanar da shi idan bai sani ba, idan ya ci gaba da inkarinta to shi kafiri ne, mai qaryata Allah da Manzonsa da haxuwar Musulmai.

2 – Wanda Ba Ya Sallah Saboda Kasala :

Wanda ya bar sallah da gangan saboda kasala ya kafirta, wajibi ne akan shugaba ya kira shi zuwa ga yin sallah, ya bijirar masa da tuba, har tsawon kwana uku, idan ya tuba shike nan, in kuwa bai tuba ba, shugaba ya kashe shi a matsayin kafiri wanda ya yi ridda, saboda faxin Manzon Allah (S.A.W) “Alqawarin da yake tsakaninmu da su shi ne sallah, duk wanda ya bar ta haqiqa ya kafirta” [Tirmizi ne ya rawaito shi].
Da faxinsa (S.A.W) “Tsakanin mutum da shirka da kafirci shi ne barin sallah” [Muslim ne ya rawaito shi].
Sallar qaramin yaro
Qaramin yaro ana umartar sa da yin sallah idan ya kai shekara bakwai, don ya saba da ita. Ana dukansa a kanta idan ya kai shekara goma, dukan da ba mai ciwo ba. Manzon Allah (S.A.W) ya ce, “Ku umarci ‘ya’yanku da sallah, suna ‘yan shekara bakwai, ku dake su a kanta suna ‘yan shekara goma” [Abu Dawud ne ya rawaito shi].
source@www.al-feqh.com
Read More

Yadda Ake Yin Sallar Jana’iza

January 01, 2019 0
YAN-UWA Mafi yawancinmu, muna yin Sallar Jana’iza amma kuma ba mu san abinda ake fada a cikin kowacce Kabbara ba. Dan hak shi yasa na ga cewa yana da kyau in ware mana wani lokaci na musamman, Domin in fahimtar
da mu yadda ake yin sallar Jana’za.

Image result for sallar gawa
‘YAN-UWA ita dai Sallar janai’za, tana da babban lada, ga wanda ya aikata
ta kamar yadda Manzon Allah (SAW) ya koyar, dan haka yana da kyau, mu tsaya mu koya.
Kamar yadda na ce, sallar jana’za tana da kabbarori guda hudu ne
kawai kuma kowacce Kabbara da abin da ake fada a cikinta.
1. KABBARA TA FARKO ana karanta {suraul-fatiha} ne kawai, banda wata sura, ko wata a’ya.
2. KABBARA TA BIYU ana karanta Salatin Annabi ba wani salati na daban ba.
3. KABBARA TA UKU ana yin addu’a ga wanda ya mutu mace ko namiji.
4. KABBARA TA HUDU za ka yi addu’a ne a kanka da sauran al’ummar Musulmi.
DAN UWA KANA GAMAWA sai ka jira Liman ya yi sallama. Ita kuma sallamar guda daya ce tak! Kuma za ka yi ta ne a bangaren damanka.
Allah muke roko da ya kara tabbatar damu akan Sunnar Annabin Rahama, Manzon Allah (S.A.W).
Akwai bukatar a yada domin ‘yan uwa musulmai su karu.
source@http://fiqhussunnah.blogspot.com
Read More

Post Top Ad

Mediaofislam.com